An kama mai maganin gargajiya kan kisan ɗaliba a Edo
Marigayiyar ta ɓace tun a ranar 4 ga watan Afrilu a unguwar Iru Egbede da ke ƙaramar hukumar Orhionmwon ta Jihar Edo.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo sun kama wani mai maganin gargajiya ɗan shekara 26, Chukwuyem Jonah, da wasu mutum biyu bisa zargin kashe wata ɗalibar aji biyu a Jami’ar Jihar Delta, Misis Faith Omodon.
An bayyana cewa marigayiyar ta ɓace ne a ranar 4 ga watan Afrilu a unguwar Iru Egbede da ke Ƙaramar Hukumar Orhionmwon ta Jihar Edo bayan ta je gona ba ta dawo ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Funsho Adegboye ya bayyana sunayen ababen zargin da suka haɗa da Godspower Chukwuedo mai shekara 23 da kuma Christopher Nwachukwu mai shekara 22 a lokacin da yi wa manema labarai holen waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban a jihar.
Mahaifin marigayiyar, Edward Omodon ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
“Na san Chukwuyem Jonah sosai; mun zauna tare. Ina ganinsa kowace rana,” in ji shi.
“Ina son a yi wa ’yata adalci. Ina so su biya kuɗin diyyar kashe ’yata. Ba na son ’yata ta mutu haka ba tare da mahukunta sun ɗauki wani mataki ba,” in ji shi.