An kama mai mata biyar a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wani mutum da ya auri mata biyar a lokaci guda, inda har ta tilasta shi sakin daya daga ciki.Mutumin, wanda aka boye sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa kuskure ne ya kai shi ga aikata wannan lamari, inda kuma ya yi alkawarin ba zai sake aikata makamancin hakan […]

An kama mai mata biyar a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wani mutum da ya auri mata biyar a lokaci guda, inda har ta tilasta shi sakin daya daga ciki.
Mutumin, wanda aka boye sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa kuskure ne ya kai shi ga aikata wannan lamari, inda kuma ya yi alkawarin ba zai sake aikata makamancin hakan a nan gaba ba. “Babu shakka hakan ya faru, an same ni da laifin auren mata biyar, sai dai na aikata wannan abu ne bisa kuskure. Kasancewar ba a gida daya dukkanin matan suke zaune ba, hakan ya sa ban iya tantance yawansu ba. Amma ina rokon afuwa, ba zan sake aikata irin hakan a nan gaba ba”. Inji shi.
Su ma matan wannan mutumin su biyar, wadanda aka tara su a hukumar ta Hisba, sun bayyana wa Aminiya cewa ba su san cewa haka abin yake ba, sai yanzu da aka kawo su saboda boye musu aure na biyar din da maigidan nasu ya yi. “A gaskiya ba mu san cewa mu biyar ne a wurin mijinmu ba sai a yanzu, kasancewar ba a gida daya dukkaninmu muke zaune ba, mu biyu ne kawai a gida daya, yayin da sauran suke a gidaje daban-daban. A kwanakin baya mutane sun rika kawo mana tsegumi a kan hakan, inda muka dauka jita-jita ce”. Inji uwargidan mutumin.
Barista Nabahani Usman, wanda shi ne Mataimakin Kwamandan Hisba, bangaren ayyuka na musamman, ya bayyana wa Aminiya cewa Hukumar Hisba ta tilasta wannan mutumi ya saki mace guda daga cikin matan guda biyar, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. “Lokacin da muka kama wannan mutumi mun kai shi gaban Babban Kwamandan Hisba inda ya amsa laifinsa, a nan take Kwamanda ya umarce shi ya saki mace guda daga ciki, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sannan aka kuma gargade shi da ya guji aikata hakan a nan gaba, domin addinin Musulunci bai ba wa namiji damar auren mace fiye da hudu ba. Wanann ketare iyaka ne”. Inji Barista Nabahani.
Ita ma amaryar mutumin, wacce ba ta fi wata uku da tarewa ba, wacce kuma ita mutumin ya saki, ta bayyana cewa ta dauki lamarin a matsayin kaddara. “Ni dai babu abin da zan ce sai dai na dauki abin a matsayin kaddara wacce ta riga fata. Kuma ni ma ba ni da masaniya kan cewa ni ce matarsa ta biyar, saboda ya gaya min cewa mata uku gare shi.” Inji sakakkiyar amaryar mutumin.
Idan dai za a iya tunawa, wanan ba shi ne karo na farko da ake samun mazan da ke ketare iyaka suna auren mata fiye da hudu ba, domin ko a kwanakin baya ma an samu wani mutum da ya auri mata tara a Ungogo cikin Jihar Kano, baya ga shahararren mutumin nan da ke da mata 86 a Bida ta Jihar Neja, wato Bello Masaba.