An kama mai mata shida a Kano

Hukumar Hisba a karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da auren mata shida a Unguwar Hotoro da ke birnin Kano. Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya ce Kotun Shari’ar Musulunci ta Unguwa uku […]

An kama mai mata shida a Kano
An kama mai mata shida a Kano

Hukumar Hisba a karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da auren mata shida a Unguwar Hotoro da ke birnin Kano.

Da yake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya ce Kotun Shari’ar Musulunci ta Unguwa uku ce ta tura musu shi don gudanar da bincike.
Mai mata shidan wanda aka boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa aikin Shaidan ne ya kai shi ga samun kansa a cikin wannan yanayi kasancewar yana sane da haramcin auren mata fiye da hudu a Musulunci.
Ya yi da nasanin abin da ya aikata tare da neman hukuma ta yi masa sassauci cikin hukuncin da za ta yi masa. “Na gane kuskurena amma ina nemna hukuma ta yi min sassauci ba zan sake maimaita hakan a nan gaba ba. A yanzu haka ma na dauki matakin rabuwa da biyu daga cikin matan nawa,” inji shi.
Uwargidan mutumin ta bayyana wa Aminiya cewa a iya saninta su hudu ne matan maigidan nata saboda su hudu suke tare a gida daya. “Wallahi ban san cewa yana da wasu matan biyu a wani gidan daban da namu ba. A iya sanina mu hudun da muke tare gida daya mu ne kawai matansa,” inji ta.
Ita ma amaryarsa wacce ita ce ta shida a wurinsa ta ce mijin nata ya yi mata karyar cewa matarsa daya ce rak inda kuma ya hada su a gida daya, “lokacin da ya aure ni ya gaya min yana da mata daya shi ne ya hada mu gida daya da ita. Ban san cewa yana da wasu matan har hudu ba,” inji ta.
ASP Majiya ya ce tunda sun kamamla bincike a kan mutumin har kuma sun samu nasarar gano dukkan mata shidan za su mayar da batun gabn kotun don yanke hukuncin da ya
dace da shi. “Kamar yadda kuke gani ga dukkan matan shida a gabanmu, don haka abin da ya rage shi ne mu mayar da batun gaban Kotun Shari’ar Musulunci wadda tun farko ita ta turo mana batun don gudanar da bincike. Kotun ce ke da hurumin yanke masa
hukuncin da ya dace da shi bisa koyarwar addinin Musulunci,” inji Majiya.