An kama mai neman sarauta da takardar WAEC ta bogi
Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama daya daga cikin ’yan takarar sarautar Oba na Iwoye a yankin Ilaro a jihar, bisa zarginsa da mallakar takardar kammala karatun sakandare (WAEC) ta bogi. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa jami’an su sun kama wanda ake zargin mai suna Alhaji […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta kama daya daga cikin ’yan takarar sarautar Oba na Iwoye a yankin Ilaro a jihar, bisa zarginsa da mallakar takardar kammala karatun sakandare (WAEC) ta bogi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa jami’an su sun kama wanda ake zargin mai suna Alhaji Fagbemi Waheed, bayan takardar koke da tsangayar lauyoyi ta R.R.A ta shigar ga rundunar a kan wanda ake zargin, inda ta ce ya mallaki takardar kammala karatun sakandare ta bogi mai lamba NGSG 809573 wacce ya ce an ba shi a 1988. Kungiyar ta ce ya mallaki takardar ce domin ya tsaya takarar sarautar Oba na Iwoye da ita.
Ya ce, bayan da rundunar ’yan sandan ta karbi koken ta samu takardar izinin bincikar gidan wanda ake zargin daga kotun, sai ta gano takardar shaidar kammala karatun sakandaren ta kuma kama wanda ake zargin kuma binciken da aka yi ya nuna cewa, asalin mai takardar shaidar karatun wata mace ce mai suna Riamot Omotola Adebayo. “Ya shaida mana cewa, ya karbi takardar shaidar ce a wajenta da zimmar zai samar mata aiki, sai ya kai takardar madabba’a aka yi masa kwafinta aka sanya sunansa, a yunkurinsa na yin amfani da takardar sarautar da yake buri,” inji shi.