An kama mai satar bayanan katin ATM a Dubai
Jami’an ’yan sandan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sun yi amfani da masu lekern asiri wajen kama wani mutum da ake zar gi da amfani da na’urar kyamara wajen satar bayanan sirri daga katunan mutane da suke zurawa a na’urar daukar kudi (ATM), inda aka kama shi dumu-dumu a Dubai.Mutumin da ake tuhuma dan kasar Bulgeriya, […]
Jami’an ’yan sandan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sun yi amfani da masu lekern asiri wajen kama wani mutum da ake zar gi da amfani da na’urar kyamara wajen satar bayanan sirri daga katunan mutane da suke zurawa a na’urar daukar kudi (ATM), inda aka kama shi dumu-dumu a Dubai.
Mutumin da ake tuhuma dan kasar Bulgeriya, ya tsere daga Daular Larabawan bayan da ya saci kimanin Dirhami dubu 200, wato daidai da Naira miliyan takwas. Mutumin yana yin satar ne ta hanyar amfani da bayanan sata da ya tattara daga katunan mutane da suke zurawa a na’urar ATM. An kama mutumin ne bayan da aka yaudare shi ya dawo Dubai.
Mutumin da ake zargi, kyamarar CCTb da ake amfani da ita wajen tattara bayanan tsaro ta dauki hotonsa a yayin da yake cire kyamarar da ya makala a jikin na’urar ATM, don ta tattara masa sirrin katin mutane da ke zurawa.
Manjo-Janar Khalil Ibrahim Al Mansouri, mataimakin Shugaban Hukumar ’Yan sandan Birnin Dubai masu binciken miyagun laifuffuka, ya ce sun samu dimbin korafe-korafe daga mutane kan yadda ake cire musu kudi daga asusun ajiyarsu. A daukacin korafin da aka kawo, an fahimci cewa, ana zare wa mutanen kudinsu bayan sun cire kudi daga na’urar ATM.
A da ’yan sanda sun dauka yana zare kudin ne ta hanyar satar katin zaro kudi daga ATM, amma sai suka fahimci lamarin ba haka yake ba.
Manjo Salah bn Osaiba, Darakta Sashen Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati na Dubai, ya shawarci mutane da su rika yawan sauya lambobin sirri da suke amfani da su wajen zarar kudi daga ATM. Sannan ya shawarci mutanen birnin da su daina yin ciniki a shafukan kasuwanci na intanet da ba a tantance sahihancinsu ba.