An kama mai sayar da jabun Dalar Amurka a Gombe
Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Gombe ta ce ta samu nasarar kama wani da ake zargin ya na sayar da jabun takardun Dalar Amurka mai suna Augustine Samuel. Kakakin Hukumar, Buhari Sa’ad ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a Gombe a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce an […]
Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jihar Gombe ta ce ta samu nasarar kama wani da ake zargin ya na sayar da jabun takardun Dalar Amurka mai suna Augustine Samuel.
Kakakin Hukumar, Buhari Sa’ad ne ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema labarai a Gombe a ranar Talatar da ta gabata.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan da aka samu bayanan sirri kan ainihin abin da yake aikatawa daga wadansu jama’a. Ya ce an kama wanda ake zargin dauke da takardun Dalar Amurka guda 30, wadda kowace daya Dala 100 ce.
Daga nan sai ya ce yawan safarar jabun Dala da yadda ake bayar da jabunta, abin damuwa ne kwarai a jihar. Yana mai cewa hukumar tasu za ta kara tashi tsaye domin magance wannan matsala.
Kakakin ya ce ana ci gaba da bincike, kuma nan ba da dadewa ba za a gabatar da wanda ake zargin, mai shekara 46 a gaban kotu. Ya kuma yi kira ga jama’a su ci gaba da ba su hadin kai domin a kakkabe bata-gari daga cikin al’umma.