An kama mai sayen katunan zabe a Taraba

Dubun daya daga cikin wadanda ake zargi da sayen katunan zabe daga hannun jama’a a Jihar Taraba ta cika, bayan da ’yan sanda suka kama shi a garin Tella da ke karamar Hukumar Gassol da ke jihar. Wanda ake zargin mai suna Habu an kama shi ne a garin Tella da katunan zabe fiye da […]

An kama mai sayen katunan zabe a Taraba
An kama mai sayen katunan zabe a Taraba

Dubun daya daga cikin wadanda ake zargi da sayen katunan zabe daga hannun jama’a a Jihar Taraba ta cika, bayan da ’yan sanda suka kama shi a garin Tella da ke karamar Hukumar Gassol da ke jihar.

Wanda ake zargin mai suna Habu an kama shi ne a garin Tella da katunan zabe fiye da 50 wadanda ake zargin ya saya ne a hannun jama’ar yankin.
Kama Habu ya biyo bayan wani samame da ’yan sanda a yankin suka yi bayan an kai musu tsegumin hada-hadar sayen kati da ke gudana a yankin inda kuma suka same shi da katunan.
Dama al’ummar karamar Hukumar Gassol sun yi kukan cewa wasu mutane suna bi gida-gida suna sayen katunan zabe a hannun jama’a.
Binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa wanda aka kama ya sayi kowane kati daya ne a kan sama da Naira dubu goma. Kuma an ce wasu manyan ’yan siyasa ne suka fidda makudan kudi don sayen katunan daga hannun magoya bayan wata jam’iyyar adawa.
Wata majiya a yankin ta shaida wa wakilinmu cewa wanda aka kama sannan ne a yankin kuma har yana bugun kirji yana cewa ya sayi gida da kudin da ya samu daga wannan cuwa-cuwa.
Majiyar ta ce tuni ’yan sanda suka tasa keyar wanda aka kama zuwa hedkwatar ’yan sandan jihar da ke Jalingo don ci gaba da bincike.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba ASP Joseph Kwaji ya tabbatar da kama wanda ake zargin.
Idan ba a manta ba kwanakin baya jaridar Aminiya ta bayar da rahoton bayyanar wasu mutane da ake zargi da sayen katunan zabe a wasu yankunan Jihar Taraba.