An kama mai shayarwa ta kai miyagun kwayoyi ofishin NDLEA

NDLEA ta kama matashi da takarda dubu 10 na kwayar Tramol a Kano.

An kama mai shayarwa ta kai miyagun kwayoyi ofishin NDLEA

Jami’an hukumar NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama wani matashi dauke da katuna dubu 10 da 161 na kwaywar Tramol da sauransu a Jihar Kano.

An kama matashin mai shekara 45, wanda kuma dilan miyagun kwayoyi ne, a kan hanyarsa ta zuwa raba kyawoyin ga abokan huldarsa.

Kakakin NDLEA na Kasa, Femi Babafemi, ya ce hukumar ta kama wata mace mai shayarwa tana kokarin shigar da miyagun kwayoyi cikin ofishin hukumar, wurin wani wanda hukumar take tsare da shi kan zargin ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Ya ce asirin matar ya tonu ne a wurin tantance abincin da ta kawo wa mutumin da ke tsare a ofishin hukumar a Jihar Edo, inda aka gano kulli biyu na tabar wiwi mai nauyin gram 13 a cikin malmalar tuwon Akpu.

Babafemi ya kara da cewa hukumar ta kai samame wani daji a Jihar ta Edo inda ta lalata wata gonar tabar wiwi, ta kama buhuna 100 na tabar ta kuma kama mai gonar, wadan aka samu da bubu 66 na tabar wiwi.

Hukumar ta kuma kama wasu mutum biyu da aka yiwo wa fasakwaurin hodar heroin mai nauyin kilogram hudu daga kasar Afirka ta Kudu, ta filin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.

Ta kuma dakile yunkurin fasakwaurin katon biyu na tabar wiwi masu nauyin kilogram 31 daga Najeriya zuwa kasar Birtaniya, kuma an cafke mai kayan.

A jihar Ondo, hukumar kuma an kama tabar wiwi mai nauyin kilgoram 302 a wani dakin ajiyar kaya da ke dajin Umure a jihar.

A Jihar Filato kuma wani matafiyi ne aka kama dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogram 12 da aka matse, a cikin wata mota da taso daga Legas a kan hayar Abuja zuwa Jos.

An kuma wani sojan karye ne jami’an NDLEA suka kama dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogram 11 a garin Zariya.