An kama mai shekara 15 bisa yunkurin garkuwa da dalibai a Neja
’Yan Sanda sun cafke wani saurayi mai shekara 15 kan yunkurin yin garkuwa da wasu dalibai a wata makaranta a Karamar Hukumar Gurara ta Jihar Neja. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Adamu Usman ya ce yaron wanda dan aji biyun karamar sakandare ne dalibi ne a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Izom. Za a fara […]
’Yan Sanda sun cafke wani saurayi mai shekara 15 kan yunkurin yin garkuwa da wasu dalibai a wata makaranta a Karamar Hukumar Gurara ta Jihar Neja.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Adamu Usman ya ce yaron wanda dan aji biyun karamar sakandare ne dalibi ne a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Izom.
- Za a fara yanke wa masu fyade hukuncin kisa a Jigawa
- Abin da ya sa na dade ana damawa da ni a Kannywood —Aminu Saira
Kwamishinan ya ce, dalibin ya rubuta wasika ya kuma kafe ta a allon sanarwar makarantar, inda a cikin wasikar yake sanar da ma’aikata da dalibai kudurinsa na satar daliban makarantar.
Bayan da aka tistiye shi, dalibin ya bayyana cewa ya rubuta sakon ne don ya tayar da hankalin ma’aikata da daliban makarantar saboda a rufe ta.
Usman, ya ce tuni an girke jami’an tsaro a makarantar don tabbatar da tsaron lafiyar malamai da daliba.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba kan duk wata alamar rashin tsaro; Babban manufarmu ita ce tabbatar da daukar duk matakan da suka dace kan sha’anin tsaro,” inji shi.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce rundunar ta riga ta fara bincike kan lamarin sannan ya bukaci jama’a da su ba da gudunmuwa ta hanyar ba wa da jami’’n tsaro bayanai masu alaka da ’yan bindiga da sha’anin tsaro don kawo karshen garkuwa da mutane a fadin Jihar.