An kama mai shekara 70 kan luwadi da yaro mai shekara 12
Dubun wani tsoho mai shekara 70 ta cika bayan ya yi luwadi da wani yaro mai shekara 12 a yankin Zariya, Jihar Kaduna.
Dubun wani tsoho mai shekara 70 ta cika bayan ya yi luwadi da wani yaro mai shekara 12 a yankin Zariya, Jihar Kaduna.
Bayanai daga mazauna yankin Kwantiresha Dogara ta Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, sun ce cewar wannan ba shi ne karon farko da tsoghon yake aikata irin wannan ta’asa ba.
’Yar uwar yaron da aka bata ta shaida wa Aminiya cewa tsohon ya yaudari yaron ne cewa ya zo su je gidansa da yake ginawa ya debo wa mahaifiyarsa zogale — ta haka ne ya yaudari kanin nata har ya kai shi wannan gidan ya bata shi.
Ta ce bayyan kanin nata ya dawo gida ne sai mahaifiyar taga yana kuka, kafin a tambaye shi ya yi bayanin abin da ya faru da shi.
Daga nan aka kai maganar wajan ’yan sanda, aka kai Asibiti aka duba shi kuma aka bashi magungunan.
Ta shaida wa wakilinmu a lokacin da suke tattauna an kira su domin a tora su zuwa ofishin ’yan sanda.
Shugaban ’yan sanda yakin Sabon Gari ya tabbatar da kama tsohon da kuma tasa keyarsa zuwa Sashen binciken manyan laifuffuka ta jiha don kammala bincike.
Duk kokarin jin tabakin kakakin mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, bai yi nasara ba — har muka kammala hada wannan rahoton bai dauki waya ba.