An kama mai shirin tada bam a Toro

Wani da ake zargin dan Boko Haram ne ya shiga hannu a garin Narabi da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi bayan da aka kama shi da harsasai 287 da bama-bamai da hijabi a lokacin da ya tambayi inda babban masallacin garin yake.  Majiyarmu ta ce ganin yadda ake fuskantar hare-haren bama-bamai sai ’yan […]

An kama mai shirin tada bam a Toro
An kama mai shirin tada bam a Toro

Wani da ake zargin dan Boko Haram ne ya shiga hannu a garin Narabi da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi bayan da aka kama shi da harsasai 287 da bama-bamai da hijabi a lokacin da ya tambayi inda babban masallacin garin yake. 

Majiyarmu ta ce ganin yadda ake fuskantar hare-haren bama-bamai sai ’yan banga suka sha jinin jikinsu inda suka kama shi inda suka gano wadannan abubuwa da aka ambata, kuma da suka binciki wayar hannunsa sai suka ga an tura masa sakon aike masa da Naira miliyan biyu cikin asusunsa na banki.
An garzaya da shi ofishin shiyya na ’yan sanda da ke Toro don ci gaba da bincike kafin a mika shi ga hedkwatar ’yan sanda da ke Bauchi.
Sai dai a sakon tes da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Mohammed ya aiko wa Aminiya bayan ta nemi bayani daga gare shi, ya ce ’yan sanda da ’yan banga da suke sintirin hadin gwiwa ne suka kama wanda ake zargin mai suna Mohammed Abdullahi, mai kimanin shekara 28 wanda ya fito daga Bajoga a Jihar Gombe, a daidai lokacin da sama da mutum dubu daya suke kokarin hallaka shi.
Ya ce kayayyakin da aka samu a tare da mutumin sun hada da harsasai biyu masu rai da katin dan kasa guda biyu daya na wani mai suna Shiga Abel danjuma daya na Umaru Hamisu.
Sauran sun hada da takardun cire kudi biyu na asusun ajiyar banki na bankin Eco Bank dauke da sunan Mohammed Abdullahi Sale da Alhassan Inusa Abdu, sai kuma takardar shaidar wanda ake zargin da katin cire kudi ATM dauke da sunansa da katin waya uku na airtel da daya na MTN. Sai kuma hijabi na mata guda daya da takardar Naira 500 da ake zargin ta jabu ce.
Ya ce suna gudanar da bincike a kan lamari tare da sanya ido kan yadda al’amura suke gudana.