An kama majinyaci kan zargin yin fyade ga ’yar wata 16 a gadon asibiti
A ranar Juma’ar da ta gabata ne da misalin karfe 2:00 na rana jami’an tsaro suka shiga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman dan Fodiyo suka kama wani majinyaci mai suna Auwal Muhammad da ke kwance a gadon asibiti kan zarginsa da yi wa ’yar wata 16 fyade a gadonsa na asibitin.Auwal mai shekara 35, wata […]

A ranar Juma’ar da ta gabata ne da misalin karfe 2:00 na rana jami’an tsaro suka shiga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman dan Fodiyo suka kama wani majinyaci mai suna Auwal Muhammad da ke kwance a gadon asibiti kan zarginsa da yi wa ’yar wata 16 fyade a gadonsa na asibitin.
Auwal mai shekara 35, wata kungiyar sa-kai ne takai shi asibitin sanadin hadarin mota da ya samu inda kashin kafarsa ya samu matsala, kuma ya fara jinya a gida kafin a garzayo da shi asibiti.
A zantawar da Aminiya ta yi wani da abin ya faru a kan idonsa ya bayyana cewa, “A ranar Juma’a da karfe 2:00 rana mahaifiyar yarinyar tare da yayanta da ke dauke da ita sun zo duba wasu ’yan uwansu da ba su da lafiya a asbitin kawai wanda ake zargi ya karbi yarinyar a hannunsa kamar zai yi mata wasa sai ya juya ya yi mata fyade a kan gadonsa na jinya. Ana haka ne mahaifiyarta ta ji karar kukanta sai ta fara kallo da bincikar inda ’yarta take inda ta gan ta majinyacin ya yi mata fyade a kwanar gadonsa da aka rufe da labule.”
Ya kara da cewa, “Da ganin haka ta yi gaggawar karbe ’yarta ta je ta sanar da jami’an tsaron asibitin inda suka zo suka kama shi zuwa ofishin ’yan sanda na Kwanni daga nan aka wuce da shi zuwa hedkwatar ’yan sanda ta Jihar Sakkwato.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Al-mustafa Sani ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da shaida masa cewa an bayar da belin wanda ake zargin har sai ya samu saukin rashin lafiyarsa.