An kama ‘makudan’ kudin jabu a Nijar

A shekaranjiya Laraba ne jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar suka ce sun kai samame wani waje, inda suka kwace ‘makudan kudin’ jabu na kasashen ketare, kamar yadda BBC ta bayyana.Gidan talabijin gwamnatin kasar ta ambato jami’an tsaron suna cewa sun kwace akalla CFA 270m da euro da kuma daloli na jabu a garin Takieta na […]

An kama ‘makudan’ kudin jabu a Nijar
An kama ‘makudan’ kudin jabu a Nijar

A shekaranjiya Laraba ne jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar suka ce sun kai samame wani waje, inda suka kwace ‘makudan kudin’ jabu na kasashen ketare, kamar yadda BBC ta bayyana.
Gidan talabijin gwamnatin kasar ta ambato jami’an tsaron suna cewa sun kwace akalla CFA 270m da euro da kuma daloli na jabu a garin Takieta na yankin Zinder.
Hakazalika, jami’an sun ce sun kwato fasfo-fasfo da takardun motoci da lasisi na jabu.
Sai dai jami’an sun ce mutanen da ake zargin da hannu a wajen ajiye kayayyakin jabun sun tsere, suna masu cewa sun samu makamai uku a wajen.
Dokar Nijar dai ta tanaji daurin shekaru 10 a gidan yari a kan duk wanda aka samu da laifin ta’ammali da takardun jabu.