An kama malama tana lalata da ɗalibinta

Har yanzu dai ba a tabbatar da halin da take ciki a gidan yari ba. Babu tabbas ko Flores za ta daukaka kara.

An kama malama tana lalata da ɗalibinta

An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17.

Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar.

An kama malama Dulce Flores, mai shekara 28 bayan da ta kulla dangantakar da ba ta dace ba da wani dalibi dan shekara 17 a makarantar sakandare ta Riberbank a 2023, a cewar ’yan sandan Riverbank.

Malamar wacce take koyar da harshen Sipaniya tana aiki a makarantar tun 2016.

Haka kuma a cewar shafinta na LinkedIn, ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan kyau ga wani kamfani na kayan kwalliya.

A wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta ce, an fara gudanar da binciken ne bayan wani jami’in makarantar ya samu labarin alakar malamar da dalibin.

An kama Flores a cikin gidanta, inda aka tuhume ta da laifin yin lalata da karamin yaro ba bisa ka’ida ba, in ji ‘yan sanda.

Gundumar makarantar a baya ta bayyana wa jaridar The Modesto Bee cewa, za su hada kai da masu bincike idan akwai bukatar hakan kuma sun bai wa Flores hutu har sai an gama gudanar da bincike.

Mahukuntan makarantar sun ci gaba da cewa, za su yi magana da iyaye da daliban da suka yi rajista a azuzuwan Flores.

A cikin wata sanarwa, Sufeto Constantio Aguilar ya ce: ‘Abin takaici ne ga gundumarmu ta fuskanci yanayi irin wannan.

Yayin da muke ci gaba da yin aiki tare da jami’an tsaro, gundumar kuma za ta duba don tantance irin matakan da za ta iya bi don magance lamarin.’

Gundumar ta kara da cewa, ba ta tsammanin komai sai mafi kyawun inganci da kwarewar ma’aikatansu.’

An tsare Flores a gidan yari na Stanislaus County da neman beli a kan Dalar Amurka 20,000 bayan da wakilin gundumar suka samu sammacin kama ta.

Ofishin gundumar yankin Sheriff ya gode wa mahukuntar makarantar sabda ‘ba da rahoto cikin gaggawa’ da hadin kai wanda ‘ya taimaka wa masu bincike don tantance yanayin lamarin.’

Har yanzu dai ba a tabbatar da halin da take ciki a gidan yari ba. Babu tabbas ko Flores za ta daukaka kara.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kama wani ma’aikacin makarantar sakandaren Riverbank da laifin yin lalata da wani dalibi ba.

A shekarar 2023 makarantar sakandare ta Riverbank ta fada cikin irin wannan yanayi bayan da aka zargi wani tsohon kocin kwallon kwando mai shekara 23 a lokacin da yin lalata da wani matashi dan shekara 16.

Logan Navors na fuskantar tuhumetuhume da suka shafi lalata da karamin yaro.

An gurfanar da Navors a gaban kotu a watan Satumba, amma ba a sani ba ko ya daukaka kara a wannan lokacin.