An kama malami da yi wa daliba fyade a aji

Ana zargin wani malamin makarantar boko, mai suna Alaga Solomon Ari da yi wa dalibarsa ’yar shekara 15 fyade a aji a Jihar Nasarawa. Wannan lamarin ya faru ne a Makarantar Mishan ta Sudan United Mission (S.U.M) da ke garin Agwatashi a karamar Hukumar Obi da ke jihar. Dalibar wacce aka sakaya sunanta ta ce […]

An kama malami da yi wa daliba fyade a aji

Ana zargin wani malamin makarantar boko, mai suna Alaga Solomon Ari da yi wa dalibarsa ’yar shekara 15 fyade a aji a Jihar Nasarawa.

Wannan lamarin ya faru ne a Makarantar Mishan ta Sudan United Mission (S.U.M) da ke garin Agwatashi a karamar Hukumar Obi da ke jihar.

Dalibar wacce aka sakaya sunanta ta ce malamin ya umarce ta ta shiga cikin aji ta dauko tsintsiya yayin da ta shiga sai ya yi wuf ya bi ta, sa’annan ya yi mata fyade inda ya ji mata ciwo.

Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muhammad Iyamoga, ya hori jama’a su guji  karya doka, inda ya ce “doka za ta yi aikinta”.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin.

“An sanar da mu cewa wani mai suna Alaga Solomon Ari ya yaudari dalibarsa ’yar shekara 15 ranar 14 ga Agustan nan; sa’annan ya yi mata fyade inda jami’anmu suka kama shi.

“Kwamishinan ’Yan sanda, Bola Longe ya umarci a mayar da binciken daga Karamar Hukumar Obi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka  (CID) da ke Lafiya”, inji shi.