An kama malami ya yi garkuwa da dalibinsa

’Yan Sandan a Jihar Ogun sun damke wani malami, Odugbesan Ayodele Samson, bisa zargin garkuwa da dalibinsa mai shekara takwas. Wanda ake zargin ya sace karamin yaron ne ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba ya kuma nemi kudin fansa N200,000 daga mahaifiyar yaron. An yi garkuwa da mashawarcin Gwamnan Sakkwato ’Yan matan da ke yunkurin […]

An kama malami ya yi garkuwa da dalibinsa

Jami’an Yan sanda

’Yan Sandan a Jihar Ogun sun damke wani malami, Odugbesan Ayodele Samson, bisa zargin garkuwa da dalibinsa mai shekara takwas.

Wanda ake zargin ya sace karamin yaron ne ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba ya kuma nemi kudin fansa N200,000 daga mahaifiyar yaron.

Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan Sanda a Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce mahaifiyar yaron, Fatimat Akeeb, ta kai kara cewa an sace danta daga makaranta a yankin Arifanla na Akute.

Mahaifiyar yaron ta ce daga baya wanda ake zargin ya kira ta a waya ya kuma umurce ta da ta biya N200,000 don a saki danta.

Oyeyemi ya ce nan take ’yan sanda suka fara binciken har suka kai ga gano maboyar wanda ake zargin.

“Don kar a cutar da yaron, an yaudari wanda ake zargin tare da biyan wani kaso na fansan sannan daga baya aka cafke shi ya kai ’yan sanda inda ya ajiye yaron wanda aka ceta ba tare da rauni ba”, in ji Oyeyemi.

Ya ce da aka titsiye wanda ake zargin, ya amsa aikata laifin amma ya ce aikin shaidan ne.

Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar, Edward Awolowo Ajogun, ya ba da umarnin a tura wanda ake zargin zuwa sashin yaki da satar mutane na sashin binciken manyan laifuka don kammala bincike da kuma gurfanar da su a kotu.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7