An kama malami yana luwadi da dalibansa

Hukumar Yaki da Safarar Mutane (NAPTIP) ta kama wani matashin malami a Jihar Kano da zargin yi wa dalibansa maza fyade ta hanyar ludu. Jami’in NAPTIP mai kula da shiyyar Kano, Shehu Umar ya ce an kama mutumin ne bayan samun rahoto cewa ya yi luwadi da kananan yara dalibai a Unguwar Kadawa, Kwanar Dillalai […]

An kama malami yana luwadi da dalibansa

Hukumar Yaki da Safarar Mutane (NAPTIP) ta kama wani matashin malami a Jihar Kano da zargin yi wa dalibansa maza fyade ta hanyar ludu.

Jami’in NAPTIP mai kula da shiyyar Kano, Shehu Umar ya ce an kama mutumin ne bayan samun rahoto cewa ya yi luwadi da kananan yara dalibai a Unguwar Kadawa, Kwanar Dillalai a ranar Talatar da ta gabata.

“Bayan samun rahoton ne muka yi maza muka dauki matakin tsare wanda ake zargin da kuma ceto wadanda ya lalata din su biyu”, inji shi.

Jami’in ce ya hukumar ta kammala bincike a kan mutum wanda ya shekara bakwai yana koyarwa a matsayin malamin addini, za ta kuma gurfanar da shi a kotu.

Ya yi kira ga al’umma musamman iyaye da su rika kulawa tare da tabbatar da sanin wuraren da kuma halin da ’ya’yansu ke ciki a kowane lokaci musamman almajirai.

An kama mai safarar mutane

Shehu Umar ya ce ofishin NAPTIP na Kano ya kuma kubutar da wasu mutum shida daga hannun masu safarar mutane a jihar bayan samun bayanai kan motsin masu muguwar sana’ar.

Ya ce ofishin ya kai samame a wani otal da ke unguwar Sabon Gwari, “a ranar 23 ga watan Agusta inda aka tsare wanda ake zargin tare da kubutar da mutanen.

“An ajiye wadanda za a yi safarar nasu ne a otal din kafin a kwashe su daga Kano zuwa Libya.

“Wadanda za a yi safarar tasu sun fito ne daga jihohin Ogun, Oyo, Imo da Abia”, inji shi.

NAJERIYA A YAU: Yadda jiragen soji suka kashe fararen a karo na biyu a wata guda

Mahara sun kashe mutum 9 sun jikkata wasu a Nasarawa

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar