An kama Malamin da ke yin luwadi da dalibansa
‘Yan sanda a Jihar Sakkwato sum Kama wani malamin makaratar almajirai Malam Murtala Mode da ke Unguwar Arkillan Magaji kan zarginsa da yin luwadi da yara shida daga cikin dalibansa. Wanda ake zargin ya ce wannan kaddara ce kuma yana yi ne don ya samu kudi. A taron manema labarai Kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Ka’oje […]
Malam Murtala Mode
‘Yan sanda a Jihar Sakkwato sum Kama wani malamin makaratar almajirai Malam Murtala Mode da ke Unguwar Arkillan Magaji kan zarginsa da yin luwadi da yara shida daga cikin dalibansa.
Wanda ake zargin ya ce wannan kaddara ce kuma yana yi ne don ya samu kudi.
A taron manema labarai Kwamishinan ‘yan sanda Ibrahim Ka’oje ya ce lauya Hamza Liman na Hukumar Kare Hakkin bil adama ne ya sanar da su wanda ake zargin a caji ofis nasu da ke Arkilla.
Ya ce wanda ake zargin ya yarda ya aikata laifinsa.
Kwamishinan ya ce mafi yawan yaran suna zuwa ne daga Zamfara inda Malamin ya rika yin luwadi da su kafin asirinsa ya tonu.
Ya ce za su mayar da yaran wurin iyayensu da zarar sun kammala bincike.
Ya roki iyaye su daina tura ’ya’yansu makarantar allo a wani wuri daban da in da suke zaune.
Haka kuma Kwamishinan ya ce sun kama ‘yan banga shida a harkar fashi da makami.
‘Yan bangar sun fito ne daga Jihohin Katsina da Zamfara sun addabi kauyen Jegawa a Karamar Hukumar Kebbe an samu nasarar kashe biyu daga cikinsu a yayin da suke kokarin arcewa.
Kwamishinan ya kara da cewa sun kama wani wani Zakariyya Sani da ke Unguwar Maberar Jariri da ake zargin barawo ne da ke fasa shaguna. An gano jarkoki 20 na man girki da mota kirar Honda Cibic da babur mai taya uku da tsabar kudi Naira dubu 860 da 500, a wajensa.
Kwamishinan ya ce da zarar sun kammala bincike za a tura wanda ake zargin kotu.