An kama maniyyata dubu 300 marasa takardun aikin Hajji
Mahukuntan sun sanar da tsaurara dokoki ciki har da zaman yari ga duk wanda aka samu da aikata wannan laifi.
Hukumomi a Saudiyya sun sanar da kame maniyyata dubu 300 wadanda ba su da takardun shaidar aikin hajjin bana da ake shirin farawa a makon gobe.
A cewar Saudiya, matakin bibiyar wadanda ba su da shaidar aikin hajjin na da nufin rage cunkoson jama’a, a yayin ibadar wadda kan tattara miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya.
- Dalilin da na ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren ilimi a Kano — Abba
- Mabiya addinin gargajiya sun nemi a riƙa rantsuwa da gumakansu
Sanarwar da hukumar kula da cunkoson jama’a ta Saudiyya ta fitar ta ce cikin wadanda mutane har da dubu 153 da 998 da suka shiga kasar da takardar yawon bude ido sabanin takardar izinin aikin hajji da ya kamata su samu.
Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ce daga cikin mutanen akwai kuma wasu dubu 171 da 587 wadanda suke zaune a kasar ta Saudiyya amma ba ‘yan asalin kasar ba, kuma suka fito da nufin aikin hajjin ba tare da takardun izini ba.
Mahukuntan sun yi amannar cewa dubunnan mutane a irin wannan lokaci kan maƙale a cikin ƙasar da bizar Umrah ko kuma ta yawon buɗe ido don gudanar da aikin hajji ba tare da izini ba, wanda kuma shi ke haddasa cunkoson jama’a.
A wannan karon mahukuntan sun sanar da tsaurara dokoki ciki har da zaman yari ga duk wanda aka samu da aikata wannan laifi, sai dai duk da wannan kamen babu rahoton da ke nuna an tura mahajjatan gidan yari.