An kama manomi mai kwaikwayon sa hannu ya kwashe kudi a banki

Wani manomi, mai shekaru 54. mai suna Godwin Diabel ya shiga komar sashen ’yan sanda na musamman kan almundahana da ke titin Milberton a Ikoyi, kan almundahana yayin da aka zarge shi da satar kudin jama’a a asusunsu na banki.  Yakan yi hakan ne kuwa ta dubarar kwaikwayon sanya hannu na masu asusun ajiyar bankin.Mista […]

An kama manomi mai kwaikwayon sa hannu ya kwashe kudi a banki
An kama manomi mai kwaikwayon sa hannu ya kwashe kudi a banki

Wani manomi, mai shekaru 54. mai suna Godwin Diabel ya shiga komar sashen ’yan sanda na musamman kan almundahana da ke titin Milberton a Ikoyi, kan almundahana yayin da aka zarge shi da satar kudin jama’a a asusunsu na banki.  Yakan yi hakan ne kuwa ta dubarar kwaikwayon sanya hannu na masu asusun ajiyar bankin.
Mista Godwin dai, wanda ya yi nasarar satar kimanin Naira miliyan biyu daga asusun banki na jama’a da ke ciki da wajen Legas, dubunsa ta cika ne a yayin da ya je reshen wani bankin da ke Ogba yana son fitar da Naira dubu dari biyar (N500,000) da asusun wani mai sunan Saheed Ademola Adegbola.
A yayin da yake bayyana yadda aka cafke Godwin, kakakin sashen, Mis Ngozi Nsintume-Agu ta ce bayan da mai biyan kudi ya lura cewa hoton da ke cikin asusun ya sha bamban da na mai karbar kudi, sai ya nemi bahasi, amma Godwin bai iya bayar da amsa ba.  Ganin haka, sai aka tuntubi sashensu, lamarin da ya kai aka kama wanda ake zargin.
A watan Fabrairun da ya wuce ma, Mista Godwin, wanda dan asalin Oghare ne da ke karamar Hukumar Ethiope ta Yamma a Jihar Delta, sai da ya je reshen bankin da ke Ejigbo da sunan Peter Okoro yana neman bayani game da asusun wani mai ajiya, inda nan ma aka kama shi aka mika wa ’yan sanda.
“Haka nan a ranar 4 ga Oktobar 2013, an kama shi a reshen bankin da ke Opebi, inda ya je da sunan Samson Omobo ya nemi kwasar Naira dubu dari uku N300,000). Sannan ranar 29 ga Janairun bana, wanda ake zargin ya je reshen bankin da ke Ilupeju da sunan Sunday Onwuabaizo, inda ya yi nasarar kwasar Naira dubu dari hadu da saba’in (N470,000). Alhali a ranar 19 ga watan Nuwambar 2013, ya je reshen bankin da ke Abule Egba a matsayin shi ne Chinedu E. Onwutaly ya kwashi Naira dubu dari biyu da ashirin (N220,000). Sannan wani lokacin da ba a bayyana ba, a shekarar 2013 ya je reshen bankin da ke Abraka, inda ya yi nasarar kwasar Naira dubu dari hudu da saba’in (N470,000) a asusun wani Kabiru Mohammed Baday”. Inji ta.
A lokacin da yake ikirarin yadda yakan yi wannan aika-aika, Mista Godwin ya ce yakan je rassan bankin da dama, inda yake daukar takardun da masu asusun kan cire kudi, sai ya tafi da su gida ya yi nazarin yanayin sanya hannunsu, sannan ya kwaikwaya.
Ya ce sau da yawa yakan yi nasarar cire kudi a asusun mutane a Jihar Delta kuma ya yi nunin an taba kama shi a Opebi lokacin da yake kokarin dibar Naira dubu dari uku (N300,000) aka mika shi ga ’yan sanda.
“Lokacin da aka gurfanar da ni a kotu, sai alkalin ya kori shari’ar saboda mutanen bankin ba su zo bayar da shaida ba, kuma ba ni da asusu a bankin”, inji shi.
Mis Ngozi ta ana nan ana cigaba da bincike, kuma ana tsammanin wanda ake zargin yana cikin wata kungiya ne da suka kware wajen kwaikwayar takardun sirrin jama’a da ma gwamnati wajen yin almundahana ga jama’a da gidajen kudi.
Ta ce ana nan an himmatu wajen ganin sai an karya kashin bayan ’yan wannan kungiya, sannan da an kammala bincike za a gurfanar da shi a kotu.
Kwamishinan’yan sanda mai kula da wannan sashe na musamman, Alhaji Umar Farouk Idris ya ba masu ajiya a banki tabbacin tsayuwar dakan ’yan sanda wajen ganin an dakile masu irin wannan hali, ta yadda za su samu natsuwa wajen cigaba da gudanar da harkokinsu da bankunsu ba tare da fargaba ba.
Daga nan kuma sai ya bukaci bankuna da su rika saurin tona irin wadannan mutane kuma suna sanar da hukumar ’yan sanda a kan lokaci.