An kama manyan jami’an sojin Nijar

Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun kama akalla manyan jami’an soji hudu sakamakon wasu alamu da aka gano na yiwuwar tashin hankali a kasar, watanni biyu kafin a gudanar da babban zaben kasar.Majiyoyin soji sun ce an kama jami’an ne a ranar Talatar da ta gabata.Daga cikin wadanda ake tsare da su akwai tsohon Shugaban […]

An kama manyan jami’an sojin Nijar
An kama manyan jami’an sojin Nijar

Jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun kama akalla manyan jami’an soji hudu sakamakon wasu alamu da aka gano na yiwuwar tashin hankali a kasar, watanni biyu kafin a gudanar da babban zaben kasar.
Majiyoyin soji sun ce an kama jami’an ne a ranar Talatar da ta gabata.
Daga cikin wadanda ake tsare da su akwai tsohon Shugaban Rundunar Soji, Janar Souleymane Salou da Laftana Kanar dan Haoua, Shugaban Sansanonin Sojin Sama na Yammai, babban birnin kasar.
Kodayake, hukumomin kasar ba su bayar da wani dalili na kamun ba. An ruwaito wani dan uwan Janar Salou yana cewa, “An ce ana zarginsu da neman haddasa rigima, amma har yanzu babu wani karin bayani kan hakan.”
A ranar Talata ne gwamnatin kasar ta tsayar da ranar 21 ga watan Fabrairun badi a matsayin ranar zaben Shugaban kasa da na ’yan Majalisar Dokoki.