An kama masoya kan satar jariri a Kaduna
Kakakin ya ce da zarar sun kammala bincike za su tura waɗanda ake zargin zuwa kotu.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun kama wasu masoya biyu kan zargin satar jaririn mako shida da haihuwa a unguwar Kujama da ke Ƙaramar Hukumar Chikun.
An kama Basira Hussaini da saurayinta Sebio Samuel, kwanaki tara bayan sace jaririn.
- An kama hedimasta kan sayar da kujerun makaranta a Kano
- Hatsarin kwalekwale: Mutum 2 sun ɓace a kogin Bauchi
Basira, wadda ƙwawar mahaifiyar jaririn ce, ta amsa cewa ta ɗauke jaririn ne lokacin da ta kai wa ƙwawarta ziyara.
Ta ce ba ta ɗauki jaririn don cutar da shi ba, sai don ta yaudari saurayinta, da nufin cewae jaririn nasu ne saboda suna fama da rashin haihuwa tsawon lokacin da suka kasance tare.
“Ban ɗauki jaririn don cutar da shi ba; kawai ina so saurayina ya yarda jaririn namu ne tun da ba za mu iya haihuwa ba,” in ji Basira.
A cikin kwanakin tara da jaririn ke tare da su, Basira ta yi ƙoƙarin shayar da shi duk da ba ta da ruwan nono.
Sai dai saurayin nata ne ke bayar da kuɗi ana saya wa jaririn madara.
Sebio Samuel, ya nemi a yi musu afuwa, inda ya ce ya yi zargin Basira ƙarya ta ke masa game da cewa jaririn nasu ne tun da bai taɓa ganin ta da ciki ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Kuma ya ce waɗanda ake zargin suna hannu inda ake ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a kotu.