An kama masu buga jabun katin zabe a Jihar Nasarawa

Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (Cibil Defence) Reshen Jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane uku da take zarginsu da laifin bugawa tare da rarraba katin zabe na bogi a kofar Hausa da ke karamar Hukumar Keffi, a karshen makon da ya gabata.Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a Lafiya, Kwamandan hukumar, […]

An kama masu buga jabun katin zabe a Jihar Nasarawa
An kama masu buga jabun katin zabe a Jihar Nasarawa

Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (Cibil Defence) Reshen Jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane uku da take zarginsu da laifin bugawa tare da rarraba katin zabe na bogi a kofar Hausa da ke karamar Hukumar Keffi, a karshen makon da ya gabata.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a Lafiya, Kwamandan hukumar, Mista Andakin Moses ya bayyana cewa wasu jami’ansa ne da ke sintiri a yankin suka gano tare da cafke wadanda ake zargin.
Ya kara da cewa daga cikin abubuwa da aka gano tare da su, har da katin zabe na dindindin guda 97 da na’urori masu aiki da kwakwalwa guda biyu da kyamarori guda biyu da kuma na’urorin sikanin da dai sauransu.
Ya ci gaba da bayyana cewa shugaban wadanda ake zargin, Alhaji Muhammad Maikudi, a lokacin da yake amsa tambayoyi jami’an hukumar, ya bayyana cewa wani jami’in hukumar shirya zabe a jihar ne da aka sakaya sunansa ya biya su kudi, ya kuma tanado musu kayayyakin aiki suka gudanar da aikin.
Aminiya ta tuntubi shugaban hukumar zaben jihar, Alhaji Ahmed Muhammed Makama, inda ya bayyana cewa jami’an tsaron sun sanar da shi batun kuma a cewarsa, tuni ma ya umurci wasu jami’ansa su gudanar da cikakken bincike don gano wanda ya aikata wannan laifi. Ya kuma yi alkawarin cewa da zaran a gano shi, hukumar za ta hukunta shi daidai da laifin da ya aikata don ya kasance darasi ga sauran jami’an hukumar da ke niyyar yin haka.
An dai kammala shirin rarraba katin zabe a jihar kwanaki uku kafin aka cafke wadaannan mutane masu buga katin zaben na bogi.

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato