An kama masu damfara ta POS a gidan caca

Wasu matasa da suka damfari masu harkar hada-hadar kudi ta POS sun shiga hannun jami’an tsaro.

An kama masu damfara ta POS a gidan caca

Wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifi (Daga taskarmu).

Wasu matasa da suka damfari masu harkar hada-hadar kudi ta POS sun shiga hannun jami’an tsaro.

Dubun matasan masu shekaru 20 da kuma 28 ta cika ne bayan da sun je gidan caca da N463,000 da suka sace wa masu POS din a Jihar Neja.

Kakakin yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce an kama daya daga cikin matasan mai 20 ne bayan ya sace wata na’uarar POS a garin Mokwa, hedikwatar karar hukumar, Mokwa.

Dubunsa ta cika ne bayan da ya ciri N293,000 daga POS din da ya sato ya yi caca a kudin.

Na biyu, mai shekaru 28 da ke sana’ar POS kuma, ya fada a komar ’yan sanda ne bayan ya yi layar zana da na’urar POS da kudaden mai gidansa a garin Minna, babban birnin jihar.

Shi ma an cika hannu da shi ne bayan ya buga cacar kwallon da N170,000 da ya sace wa uban gidan nasa.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba