An kama masu garkuwa 5 da kwato shanu 115 a Filato
Hukumar ‘yan sanda ta kama mutum 5 da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne a jihar Filato, tare da kwato shanu 115. Uku daga cikin wadanda aka kama sun hada da: Abba Sa’eed, Kabiru da Abdullahi Kabiru su ne ake zargin sun yi garkuwa da wani yaro dan shekara 6 mai suna Aliyu […]
Hukumar ‘yan sanda ta kama mutum 5 da ake zargin masu yin garkuwa da mutane ne a jihar Filato, tare da kwato shanu 115.
Uku daga cikin wadanda aka kama sun hada da: Abba Sa’eed, Kabiru da Abdullahi Kabiru su ne ake zargin sun yi garkuwa da wani yaro dan shekara 6 mai suna Aliyu Aminu inda suka bukaci kudin fansa Naira miliyan 12 kafin su sako shi. Sauran biyun kuma ana zargin su ne, suka yi garkuwa da wata mata ‘yar shekara 56 da ‘yarta a Karamar Hukumar Wase ta jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato Mista Austin Agbonlahor ne ya sanar da hakan a Hedkwatar ‘yan sandan jihar da ke Jos.