An kama masu garkuwa a wurin karbar kudin fansa
Cikin masu garkuwar har da mai shekara 18.
’Yan sanda sun cafke wasu masu garkuwa da mutane a lokacin da suka je karbar kudin fansa kan wani yaro mai shekara bakwai da suka sace.
Bayan yaron ya yi batar dabo ne mahaifinsa, Stephen Ajibili, ya sanar da ’yan sanda, jim kadan bayan wadanda suka yi garkuwa da dan nasa sun kira shi ta waya, sun nemi ya biya su kudin fansa Naira miliyan daya.
- ’Yan Boko Haram na tilasta aurar da kananan yara a Neja
- Auren ‘Wuf’ ba shi da wata illa a Musulunci – Sheik Daurawa
’Yan sanda sun kama wadanda ake zargin, wadnda suka hada da wani mai shekara 18 da mai shekara 42 ne, a ranar Lahadi a Karamar Hukumar Ado Odo-Ota ta Jihar Ogun.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce an kama mutanen ne bayan ’yan sanda sun yi musu kwanton bauna a wurin da suka ce a ajiye musu kudin fansar.
Ya kara da cewa: “A lokacin binciken, wadadan da ake zargi sun tabbatar da cewa su uku ne suka yi aika-aikar, amma dayan nasu na wurin da suka daure da yaron a daji a jikin wata bishiya yana tsare da shi,” amma da ya ga abin da ya faru sai ya tsere ba a san inda ya yi ba.
Ya ce ’yan sandan za su yi iya kokarinsu waje ganin sun kamo wanda ya tseren, sbiyun da aka kama kuma an mika su zuwa ga Sashen Yaki da Garkuwa da Mutane na rundunar domin gudanar da bincike.