An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 2 A Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutum masu suna Muhammadu Garba mai shekara 25 da Ibrahim Adamu mai shekara 40 da ake zargi da yin garkuwa da wani mai suna Musa Abdullahi a Gombe. Kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a ranar 28 ga watan Satumba ne suka samu rahoton wasu […]

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 2 A Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutum masu suna Muhammadu Garba mai shekara 25 da Ibrahim Adamu mai shekara 40 da ake zargi da yin garkuwa da wani mai suna Musa Abdullahi a Gombe.

Kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a ranar 28 ga watan Satumba ne suka samu rahoton wasu mutane 14 dauke da muggan makamai da bindiga AK-47 suka shiga gidan wani mai suna Musa Abdullahi suka sace shi suka kai shi wani wajen da ba a sani ba.

Sanarwar ta ce bayan sun sace mutumin sun nemi kudin fansa Naira miliyan daya da dubu dari takwas wanda bayan sun karbi kudin kuma suka ki sakin shi.

Har ila yau ya ce wani bincike da ’yan sanda suka yi sun gano cewa wadanda ake zargin sune masu gaya wa masu garkuwa da mutane sirrin ’yan sanda.

Sun kuma tabbatar da cewa akwai wani mai suna Ya’u Saleh, shi ne asalin wanda ake zargi da garkuwan kuma abokin wanda aka sace din ne kuma sun hadu da wanda suka sace din kafin su sace shi suka gaya masa cewa suna shirin sace shi.

ASP Mahid ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike, da sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kotu.

Babban layin wutar lantarki ya faɗi karon farko a 2025

Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda

Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi

Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta

Tags