An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Sojoji sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Gubio ta Jihar Borno.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Dakarun Operation Haɗin Kai, tare da haɗin gwiwar rundunar Hybrid, sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Gubio ta Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce an kama waɗanda ake zargin ne a yammacin ranar Lahadi 21 ga watan Yuni, bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu na garkuwa da mutane a yankin.

Sun bayyana cewa dakarun Brigade ta 5 sun samar da tsaro da kuma ba da goyon baya ga rundunar Hybrid yayin gudanar da aikin, lamarin da ya kai ga nasarar gano maboyar waɗanda ake zargin tare da kama su.

Hukumomin soji sun ce an ƙwato bindigar ƙirar AK-47 guda ɗaya da kuma wasu harsasai daga hannun waɗanda ake zargin a lokacin samamen.

“An miƙa waɗanda ake zargin tare da makaman da aka ƙwato ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace,” in ji rahoton.

Rundunar Operation Haɗin Kai na ci gaba da gudanar da hare-haren da suka dogara da bayanan sirri, da nufin rage ƙarfin ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a yankin.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe