An kama masu garkuwa da mutane a tasi
Dubun wadansu mutane masu amfani da tasi suna yin garkuwa da mutane ta cika a garin Abekuta, Jihar Ogun bayan da suka shiga hannun Rundunar ’Yan sandan Jihar. Da yake yi wa ’yan jarida bayani game da mutanen su biyar tare da mace daya, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun Ahmad Iliyasu ya ce mutanen suna […]

Dubun wadansu mutane masu amfani da tasi suna yin garkuwa da mutane ta cika a garin Abekuta, Jihar Ogun bayan da suka shiga hannun Rundunar ’Yan sandan Jihar.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani game da mutanen su biyar tare da mace daya, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun Ahmad Iliyasu ya ce mutanen suna amfani da motar tasin ce, su yi garkuwa da duk wanda tsautsayi ya kama shi ya shiga motar; inda suke fesa masa wani sinadari wanda zai gusar da hankalinsa sai su karɓi katin ajiyarsa na banki, su tilasta masa ya faɗi lambar sirri na katin, su kwashe masa kuɗinsa. Haka kuma suna yi wa duk wanda ya shiga motarsu fashi, in kuma ba ya da kuɗi su yi garkuwa da shi har sai ’yan uwansa sun biya kuɗin fansa. “Jama’a su rika lura, idan za su shiga motar haya, duk motar da suka gan ta a gefen hanya cike da fasinja, aka ce su shigo daga tsakiya, su kiyaye har sai sun samu wacce ransu ya kwanta da ita,” inji shi.
Mace daya daga mutanen mai suna Misis Tajudeen Erinsho ta ce matsalar rayuwa ce ta sanya ta shiga gungun barayin. Ta ce a baya tana sayar da kayayyakin masarufi ne a ƙofar gidanta sai rayuwa ta sauya, jarinta ya karye, kasuwarta ta yanke sannan ’ya’yanta biyar.