An kama masu kera haramtattun makamai a Binuwe

’Yan sanda sun kama wasu musu uku kan zargin kerawa kuma da sayar da makamai ba bisa ka’ida ba a Jihar Binuwe.

An kama masu kera haramtattun makamai a Binuwe

’Yan sanda sun kama wasu musu uku kan zargin kerawa kuma da sayar da makamai ba bisa ka’ida ba a Jihar Binuwe.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Binuwe, Emmanuel Adesina, ya ce ana kama masu kera haramtattun makaman ne a yankin Karamar Hukumar Vandekiya.

Ya shaida wa ’yan jarida a hedikwatar rundunar a ranar Laraba cewa, “bayan samun bayanan sirri ne jami’anmu na farin kaya suka kama mutum na farko.

“A yayin bincike an gano tare da kwace kananan bindigogi uku kirar gida a hannunsa.

“Shi ne ya jagoranci jami’an namu zuwa maboyar wasu makera biyu da ke sayar masa da bindigogin da suka kera, su ma aka kama su.

“Nan gaba za a gurfanar da dukkansu a gaban kotu,” inji shi.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta