An kama masu kwacen waya 26 a Jigawa

Rundunar ta ce ta kama masu laifin ne bayan wani samame da ta kai daban-daban a jihar.

An kama masu kwacen waya 26 a Jigawa

‘Yan Sanda

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama mutum 26 da ake zargi da aikata kwacen wayoyi da kuma shan muggan kwayoyi.

Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Dutse.

Ya ce kamen ya biyo bayan wasu jerin samame da suka kai a tsakanin ranar 18 zuwa 19 ga watan Disamba, a kananan hukumomi hudu na jihar.

Kakakin ya ce jami’an rundunar sun kama wani matashi kan zargin satar waya da kuma sata kudi Naira 10,000 a garin Babura da ke Karamar Hukumar Babura.

Kazalika, sun kama wasu mutum biyu kan zargin laifin satar kwamfutoci shida da babur a Hadejia.