An kama masu satar mutane 5 da boka a Kaduna
Rundunar ta kama waɗanda ake zargin ne bayan samun bayanan sirri.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama masu garkuwa da mutane guda biyar da boka da kuma gawurtaccen ɓarawon mota.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan, ya fitar.
- Muna ɗaukar matakan kawo ƙarshen Lakurawa — Minista
- ’Yan kwangila ne dalilin ɗauke wutar lantarki —EFCC
Ya ce an kama masu garkuwa da mutanen ne, a ƙauyen Kundun a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024, bayan samun bayanan sirri.
Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama; Umar Haruna da Shu’aibu Umar da mace ɗaya mai suna Hairatu Muntari wadda ake kira da Talatu.
Ya ce rundunar ta kia samame ne ƙauyen domin kamo Umar Haruna da kuma shugaban ƙungiyarsu, wadda ta tsere.
Bincike, ya nuna cewa an gayyato Shu’aibu Umar ne domin ya shiga cikin harkar da za su gudanar a gaba.
Waɗanda ake zargin sun tabbatar da cewar suna garkuwa da mutane kafin dubunsu ta cika.
Sun kuma bayyana cewa kuɗaɗen da suka karɓa a baya daga waɗanda suka yi garkuwa da su, sun sayi masara da su, wanda tuni rundunar ta kama masarar.
Hakazalika, an kama wani mai suna Abubakar wanda ya ƙware wajen satar shanu.
Bayan shigarsa hannu an samu shanu guda takwas da tumaki takwas a wajensa.
A wani labarin kuma, a ranar 31 ga watan Oktoban 2024, wani mazaunin ƙauyen Agaji da ke Saminaka ya kai rahoton ɓacewar ’yarsa mai shekara uku a duniya.
Ya ce kwana ɗaya da ɓacewarta, aka kira shi a waya ana neman ya biya kuɗin fansa Naira biyu kafin a sake ta.
Magidancin ya biya kuɗin fansar a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2024, wanda hakan ya sa aka saki yarinyar ta koma gida.
Bayan dawowarta gida ne, jami’an tsaro suka yi bincike tare da kama wani mai suna, Osa Sa’adi wanda ya tabbatar da sace yarinyar.
An samun wayar hannu ƙirar Gionee da kuɗi Naira dubu 400 da mashin ƙirar Boxer da Keke ɗaya da kuma buhun shinkafa guda ɗaya.
Jami’an sun kuma kama mutum wani boka mai suna Mohammed Sani Usman, mai shekara 35, mazaunin ƙauyen Agaji wanda ke bayar da sa’a.
Hakazalika, kakakin rundunar ya ce sun kama wani mutum mai suna Rotimi Oyewale mai shekara 50, ɗan asalin Ejigbo a Jihar Legas, kan zargin sa da satar mota ƙirar Toyota Hilux.
Yayin bincike, ya tabbatar da cewa motar ya sato ta ne a garin Ado Ekiti kuma zai kai wa wanda zai saya a Kaduna, kan Naira miliyan 2.5.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Abdullahi, ya jinjina wa jami’an rundunar kan yadda suke nuna ƙwarewa wajen gudanar da aikinsu.