An kama masu tsafi da kokon kai da sassan jikin mutum
‘Yan sanda a jihohin Kwara da Oyo sun kama wasu mutane dauke da sassan jikin mutum na kokon kawuna da kafafu da suka tono daga makabartu domin yin tsafin kudi. Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kwara Alhaji Lawan Ado shi ne ya nuna wa ‘yan jarida wani mutumi mai shekaru 25 mai suna Olayinka Abbas […]

‘Yan sanda a jihohin Kwara da Oyo sun kama wasu mutane dauke da sassan jikin mutum na kokon kawuna da kafafu da suka tono daga makabartu domin yin tsafin kudi. Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kwara Alhaji Lawan Ado shi ne ya nuna wa ‘yan jarida wani mutumi mai shekaru 25 mai suna Olayinka Abbas Akeem da aka kama shi dauke da kokon kawunan mutane guda 7 a cikin buhu.
Kwamishinan ya shaida wa ‘yan jarida a ofishinsa a garin Ilorin cewa, mutumin ya furta da bakinsa cewa ya tono kokon kawunan ne daga makabartar musulmi ta Igbo-Owu a karamar Hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.
Ya ce, ‘yan sanda sun zage damtse wajen gano mutum na biyu da suke aikin tsafin neman kudi tare.
Da yake amsa tambayar ‘yan jarida Olayinka ya tabbatar da cewa, suna yin tsafin kudi da kokon kawunan ne tare da abokin aikinsa wanda ya tsere.
“Ya kamata jama’a su sanya idanu wajen girke masu gadi na din din din da za su rinka lura da makabartu domin gujewa aukuwar irin wannan al’amari” inji Kwamishina Lawan Ado wanda yace da zarar sun kammala bincike za su gabatar da wannan mutumi gaban kuliya manta sabo.
Shi kuwa Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo, Abiodun Odude wanda ya nuna wa ‘yan jarida mutane uku da aka kama su dauke da kokon kan mutum da kafafun mutane biyu, cewa ya yi, an kama su ne bayan sun kamala aikin tone kaburbura a makabartar Musulmi ta Isale General da ke garin Ogbomoso.
Alfa Babatunde Kareem, wanda ya jagoranci mutane biyu zuwa tonon kabarin ya shaida wa ‘yan jarida gaskiyar cewa sun aikata danyen aikin ne domin yin amfani da sassan jikin mutanen da suka tono wajen yin tsafin samun kudi.