An kama masu yi wa ’yan ta’adda safarar makamai a Kaduna
Jami’an tsaron sun samu nasarar ce bayan tare wata mota ƙirar Marsandi mai launin toka da ke hanyar zuwa Jihar Neja.
Dakarun rundunar Operation ENDURING PEACE sun kama mutum shida, ciki har da wata mace, da ake zargin suna yi wa ’yan ta’adda safarar makamai a ƙauyen Samaru da ke gundumar Zonkwa a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Polycarp Oteh, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar Litinin yayin wani samame da binciken ababen hawa, lokacin da suke taso daga birnin Jos na Jihar Filato zuwa Jihar Neja.
- Ana zargin maƙwabci da yi wa ’yar shekara 5 fyaɗe a Jos
- EU na nazarin hana yara amfani da kafafen sada zumunta
A cewarsa, jami’an tsaron sun samu wannan nasarar ce bayan tare wata mota ƙirar Marsandi mai launin toka, inda bincike ya kai ga ƙwato bindigogi uku ƙirar AK-47 da ƙananan bindigogi huɗu.
Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya yi ƙoƙarin tserewa amma aka sake cafke shi.
Rundunar ta ce an tsare waɗanda ake zargin tare da makaman da aka ƙwato domin ci gaba da bincike, tare da kira ga al’umma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai kan duk wani abu mai haifar da zargi.
