An kama masu yunƙurin daura auren jinsi a Gombe
Wasu matasa 76 da ake zargin ’yan luwadi ne da ke shirin daura auren jinshi sun fada komar hukumar tsaron farin kaya (NSCDC) a Gombe.
Wasu matasa 76 da ake zargin ’yan luwadi ne da ke shirin daura auren jinshi sun fada komar hukumar tsaron farin kaya (NSCDC) a Gombe.
Kwamandan hukumar NSCDC a Jihar Gombe, Muhammad Bello Mu’azu, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a rukunin Du’a Plaza da ke kan hanyar Gombe zuwa Bauchi bayan samun bayanan sirri kan aniyar matasan.
- Zaben Adamawa: Kotu ta dage ranar gurfanar da Hudu Yunusa
- Bayanan sahihancin takardun Tinubu sun yi karo da juna —Kotun Koli
Mu’azu ta bakin kakakin hukumar, SC Buhari Sa’ad, ya ce, “Mun kama wadanda ake zargin ne a loakcin da suke gudanar da bikin murnar zagayowar ranar haihuwar daya daga cikinsu da ya kasance dan luwadi, inda a lokacin ne suke kokarin kulla auren a tsakaninsu”.
A cewarsa, bisa rahoton da aka tsegunta musu kan hakan ne jami’ansa suka dira a wajen suka kuma yi nasarar cafke mutum 76 a cikin wadanda ake zargin.
Ya ce daga cikin mutane 76 da ake zargin, 59 maza ne, 17 kuma mata, daga cikinsu maza 21 sun furta da bakinsu cewa su ’yan luwaɗi ne, sauran kuma sun je wurin ne bisa gayyatar su da aka yi.
Muhammad Bello Mu’azu, ya ce da zarar an kammala bincike za su gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.
Ya kuma kirayi iyaye da su dinga sanya ido kan ’ya’yansu suna sanin abokansu da inda suke zuwa domin gudun lalacewar tarbiyarsu.
A zantawar sa da manema labarai, babban jigon shirya taron, wanda aka fi sani da Bushrat ya ce bikin zagayowar ranar haihuwarsa suke yi, amma aka zo aka kama su.
Mahaifinsa ya bayyana cewa ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya ɗora ɗan nasa bisa turba ta kwarai amma ya fanɗare.
Daga nan sai ya ce shi yanzu ba ruwansa, jami’an tsaro su ɗauki duk matakin da ya kamata a kansa tunda haka ya zaba wa kan sa.