An kama masu zanga-zanga kan yunkurin kone Alkur’ani a Sweden

Zanga-zangar ta biyo bayan yunkurin wata kungiya na kone Alkur’ani

An kama masu zanga-zanga kan yunkurin kone Alkur’ani a Sweden

Alkur’ani mai girma

’Yan sandan kasar Sweden sun ce sun kama mutum 26 sakamakon zanga-zangar da aka yi a wasu biranen kasar a karshen mako kan wani yunkurin wasu masu tsattsauran ra’ayi na kone Alkur’ani a kasar.

A cewar ’yan sandan, an kama takwas daga cikin masu zanga-zangar ne a birnin Norrkoping, sai 18 kuma a Linkoping, wadanda sune biranen da aka yi zanga-zangar.

’Yan sandan, a cikin wata sanarwa ranar Litinin sun ce masu zanga-zangar a birnin Norrkoping wadanda yawansu ya kai kusan 150 sun rika jifan jami’ansu da duwatsu sannan sun cinna wa motocinsu wuta.

Sun kuma ce a sakamakon taho-mu-gamar, ’yan sanda 26 da fararen hula 14 sun jikkata.

A ranar Lahadi ce dai rikici ya barke a biranen biyu a karo na biyu cikin kwana hudu, kan zanga-zangar kin jinin baki da Musulmai, wacce dan siyasar kasashen Denmark da Sweden, Rasmus Paludan, ya jagoranci shiryawa.

Hukumomin lafiya a kasar dai sun ce an kwantar da mutum 10 a asibiti sakamakon raunukan da suka samu a birnin Linkoping.

Rikicin dai ya barke ne bayan Rasmus ya shirya zanga-zangar.

Tun kusan ranar Alhamis din da ta gabata ce ’yan sanda da masu zanga-zangar suka yi ta yin taho-mu-gama, lamarin da ya kai ga jikkata mutane da kone motoci.