An kama mata 51 saboda karuwanci a titunan Abuja
’Yan sanda a Abuja sun kama wadansu mata 51 da ke tallata kawunansu da sunan karuwanci a kan titunan birnin da dare. Kamen wanda aka fara tun a ranar 24 ga watan jiya zuwa farkon makon jiya, ya hada da karin wadansu mutum 90 da gaba dayansu aka gabatar da su a gaban kotun-tafi-da-gidanta ta […]
’Yan sanda a Abuja sun kama wadansu mata 51 da ke tallata kawunansu da sunan karuwanci a kan titunan birnin da dare.
Kamen wanda aka fara tun a ranar 24 ga watan jiya zuwa farkon makon jiya, ya hada da karin wadansu mutum 90 da gaba dayansu aka gabatar da su a gaban kotun-tafi-da-gidanta ta Hukumar Kiyaye Muhalli ta birnin, kan laifin saba ka’idar birnin Abuja.
Wata majiya da ke da nasaba da hukumar ta bayyana wa Aminiya cewa aikin kamen wanda babban ofishin ’yan sanda na Wuse Zone 3 Abuja ya aiwatar, ya shafi yankin gundumar Wuse ne da ke birnin, ciki har da wadanda aka zarga da laifin aikata fasadi da suka hada da masu kwacen waya ko jakunkuna su 12 da masu sai da kayan maye 9 da ’yan Baban Bola 21, sai kuma masu lodin motoci a wuraren da aka hana, su 48.
Wadansu daga cikin wadanda aka kama an yanke masu hukuncin daurin wata 6 ko zabin biyan tarar Naira dubu 5, yayin da wadansu aka wuce da su zuwa kurkukun Keffi da ke Jihar Nassarawa don fara zama jarun.
Kakakin ’Yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Mamzah wanda ya tabbatar da lamarin ya ce za a fadada aikin zuwa duk wani sashi da aka gano ana aikata abubuwan da hukumar kula da birnin ta haramta.