An kama mata da miji masu safarar jarirai
Ma’auratan sun ce wata malamar asibiti ce ta sayar musu.
’Yan Hisbah sun cafke wata mata da mijinta da suki yiwo safarar wata jariyiya daga Jihar Delta zuwa Kano.
Jami’an Hukumar ta Jihar Kano sun cafke mata da mijin ne a tashar mota bayan da suka lura da alamar tambaya a take-taken ma’auratan.
- An kama uba yana lalata da ’yar cikinsa
- Zan kawo hargisti a zaben 2023 — Igboho
- An kama direba da ke tsafi da sassan jikin kananan yara
- Sheikh Dahiru Bauchi ya amince da nadin Sanusi Khalifan Tijjaniyya
Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Harun Ibn-sina, ya ce, “Kafin su amsa laifin safarar jaririyar, da farko ma’auratan sun yi ikirarin cewa su suka haife ta.
“Bayan da aka titsiye su, sai suka amsa cewar sayen jaririyar suka yi N900,000 a wajen wata malamar asibiti a Jihar Delta.”
Ibn-Sani wanda ya ce an kama ma’auratan ne a ranar Litinin, ya ce Hukumar ta mika su ga Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Kano don ci gaba da bincike.
Ya bukaci jama’ar jihar da su rika taimakon jami’an tsaro da bayanan sirri game duk wani abu da ba su yarda da shi ba.
Ibn-Sina, ya kuma shawarci iyaye da su rika sanya ido sosai kan ’ya’yansu don gudun fadawa hannun masu satar yara.