An kama matan da ke sanya hijabi suna sata a kasuwa
Jami’an tsaro na sibil difens sakamakon shigar burtu da suka yi suka fada shaguna sanye da hijabi a sabuwar kasuwar Dutse da nufin sayayyar Sallah amma suka bige da sata. bashine niyarsubaKawamandan Hukumar Alhaji Gidado Fari ya ce hukumar ta kama matan bisa zargin satar atamfofi da leshe-leshi da shaddoji da kayan kawa na mata […]
Jami’an tsaro na sibil difens sakamakon shigar burtu da suka yi suka fada shaguna sanye da hijabi a sabuwar kasuwar Dutse da nufin sayayyar Sallah amma suka bige da sata. bashine niyarsuba
Kawamandan Hukumar Alhaji Gidado Fari ya ce hukumar ta kama matan bisa zargin satar atamfofi da leshe-leshi da shaddoji da kayan kawa na mata da kudinsu ya ta sar wa Naira dubu 100.
Daga cikin matan da akwai Rabi Umar mai shekara 22 ’yar Unguwar Sharadda da ke Kano da Amina Aminu mai shekara 25 daga karamar Hukumar Ajingi a Jihar Kano, sai Hauwa Shehu mai shekara 23 da ta tsere kafin jami’an tsaro su kamata.
Ana zargin matan da kasancewa ’yan madigo da gudanar da karuwanci a garin Gaya da ke Jihar Kano.
Bincike ya nuna an taba kama daya daga cikinsu a bara kan zargin kokarin bata wata yarinya.
Alhaji Gidado ya ce za su gurfanar da su a gaban kotu don a hukunta su kamar yadda doka ta tanada saboda ya zama darasi ga na baya.
Can a birnin Kano kuwa Manajan Kantin Jujin Labbu, Alhaji
Umar ne ya koka inda ya ce wasu mata na bata sunan Musulunci ta hanyar sanya hijabi suna yin sace-sace a kantuna inda ya ce wasu matan sun tafka musu satar turamen zannunwa 12 masu tsada, kuma an mika su ga caji ofis na Rijiyar Zaki don bincike da gabatar da su a gaban kotu.
Ya ce matan wadanda ba yara ba ne akwai A’isha Adamu mai shekara 34 da ta ce daga Unguwa Uku take da Halima Auwalu da ta ce daga Filin Kashu na Unguwa Uku take sai kuma wata da suka dauke ta a Gyadi-Gyadi da ake ce wa Mama mai shekara 45.
A’isha Adamu ta tabbatar cewa sata suka yi kuma tun daga Unguwa Uku suka yi wa shagon na Jujin Lambu tsinke, kuma ta ce sun jima suna yin sata a kasuwanni da shaguna.