An kama matan da suka yi yunƙurin sayar da tagwayen jarirai a Legas

Uwar tagwayen jariran mata ce ta sayar wa wata ma’aikaciyar jinya saboda ba za iya ɗaukar nauyinsu ba.

An kama matan da suka yi yunƙurin sayar da tagwayen jarirai a Legas

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wasu mata biyu rungume da tagwayen jarirai ’yan kwanaki shida da haihuwa da ake zargin sun kammala cinikin sayar da su ga wata ma’aikaciyar jinya.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce jami’an ’yan sandan da ke aikin sintiri a yankin Ojodu ne suka kama kama matan a wurin tsayuwar motoci (Bus Stop) na Berger bayan samun labarin sirri daga wani bawan Allah.

Ya ce matan da aka kama rungume da tagwayen jariran sun taso ne daga Jihar Abiya a kan hanyarsu ta zuwa miƙa jariran ga ma’aikaciyar jinyar a Legas.

Ya ce matan — Ujunwa Una da Chinelo Igbechiowu — sun yi wa jami’an ’yan sanda bayanin cewa mahaifiyar jariran a Jihar Abiya ce ta yi masu alƙawarin biyansu kuɗi Naira dubu 150 a matsayin ladan aikin sufurin jariran zuwa Legas.

Haka kuma, ta tabbatar masu cewa za ta kira su ta waya domin haɗa su da ma’aikaciyar jinyar da za su miƙa wa jariran da zarar sun isa Legas.

Sun ce matar da ta haifi waɗannan tagwayen jariran mata ta sayar da ’ya’yan na ta ga jami’ar jinyar ne saboda ba za ta iya ɗaukar nauyin ɗawainiyarsu ba

SP Benjamin Hundeyin ya ce rundunar ta miƙa matan da ake zargi zuwa sashen binciken da suka shafi mata na Gender Unit domin ci gaba da binciken gano sauran masu hannu a kan lamarin.

Kazalika, ya ce tagwayen jariran an kai su gidan renon marayu domin ci gaba da kula da su.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja