An kama matar aure cikin barayin awaki a Hadeja

An kama wasu mutum uku da wata matar aure da ake zargi da satar awaki a garin Hadeja da ke Jihar Jigawa.Wadanda ake zargin da suka fada hannun jami’an tsaro, an jima ana zarginsu da satar awaki ta hanyar amfani da ganyen kuka wajen jan hankalin awakin zuwa cikin gidan wata matar aure da ake […]

An kama matar aure cikin barayin awaki a Hadeja
An kama matar aure cikin barayin awaki a Hadeja

An kama wasu mutum uku da wata matar aure da ake zargi da satar awaki a garin Hadeja da ke Jihar Jigawa.
Wadanda ake zargin da suka fada hannun jami’an tsaro, an jima ana zarginsu da satar awaki ta hanyar amfani da ganyen kuka wajen jan hankalin awakin zuwa cikin gidan wata matar aure da ake zargi uwar dakinsu ce, suna kamawa.
daya daga cikin wadanda ake zargin, wanda yaron matar ne fiye da shekara goma mai suna Malam Yahaya Hassan ya ce a baya yana sayar da dabobi ne, kuma saboda karyewar jari ya shiga satar awakin ta amfani da gidan uwar dakinsa suna sayarwa a kasuwar Gujungu da ke karamar Hukumar Gagarawa a jihar.
Hassan ya ce in ya saci awakin ya kai kasuwa ya sayar suna raba kudin ne da uwar dakinsa, wadda ita ce ta saka su a cikin harkar wato Hajiya Tabawa Adamu da danta Abba Adamu.
danta Abba Adamu ya ce mahaifiyarsa tana da masaniya kan yadda ake satar awakin, kuma ita ce take raba kudin idan Yahaya ya sayar.
Kwamanadan Hukumar Sibil Difens na Jihar Jigawa Muhammed Gidado, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce za su gurfanar wadanda ake zargin a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.
A wani labarin kuma dubun wasu matasa a Unguwar Kasuwar kofa a garin Hadeja ta cika a daidai lokacin da suka hake kofar shagon wani dan kasuwa mai suna Alhaji Muhammadu Babu-Ya-Allah suka dauke kudin adashe.
Matasan masu shekara 14 zuwa 18 ana zargin sun yi amfani da magirbi ne suka hake kofar shagon suka shiga ta kasa suka fasa wurin da yake ajiye kudi a shagon suka dauke  Naira dubu 70 na adashe da aka mai shagon ajiya, suka kai wa wani abokinsu ya ajiye musu.
Kwamandan Hukumar Sibil Difens Alhaji Muhammed Gidado ya ce Muhammed Hassan mai shekara 14 ne ya shiga shagon bayan sun hake yayin da Ibrahim Musa mai shekara 18 ya hake kofar.
Ya ce bayan kai musu rahoto ne suka shiga bincike har suka gano yaran, wadanda suka bayyana musu inda suka kai kudin suka boye. Ya ce suna ci gaba da bincike kuma da zarar sun kammala za su mika su ga kotu.