An kama matar da ke dafa wa masu garkuwa da mutane abinci a Abuja
Matar ce take yi wa masu garkuwa da mutanen cefanen kayan masarufi sannan tana dafa musu abinci tare da waɗanda suke tsare da su.
Rundunar ’Yan Sandan babban birnin Najeriya Abuja, ta cika hannu da wata mata mai juna biyu da wasu mutum uku da ake zargin suna taimaka wa masu garkuwa da mutane a yankin Bwari da ke Abuja.
’Yan sanda sun ce bincike ya nuna matar mai suna Hauwa Shafiu, ita ce take yi wa masu garkuwa da mutanen cefanen kayan masarufi sannan tana dafa musu abinci tare da waɗanda suke tsare da su.
- Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu
- Ɗan Kwankwaso ya zama ɗan takarar Mataimakin Gwamnan Kano a NDC
A cewar rundunar, waɗanda ake zargin suna cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ta kutsa cikin al’ummomin yankin domin tattara bayanan sirri da shirya hare-hare.
An kuma ƙwato babura huɗu, ƙwayoyin Tramadol, kuɗi Naira 320,000, wayoyi da sauran kayayyaki daga hannun waɗanda aka kama.