An kama matar da ta jefar da jariri a Jigawa
Jami’an ’yan sanda sun kama wata matar aure a garin Guri, Jihar Jigawa saboda zarginta da jefar da jariri a filin kwallo, lamarin da ya sa ’yan sandan suka zurfafa bincike har suka gano wadda ta haifi jaririn kuma ta jefar da shi a filin kwallon garin Abunabo. Matar mai suna Hadiza fanna, ’yar shekara […]

Jami’an ’yan sanda sun kama wata matar aure a garin Guri, Jihar Jigawa saboda zarginta da jefar da jariri a filin kwallo, lamarin da ya sa ’yan sandan suka zurfafa bincike har suka gano wadda ta haifi jaririn kuma ta jefar da shi a filin kwallon garin Abunabo.
Matar mai suna Hadiza fanna, ’yar shekara 28, ’yan sanda sun gano cewa ta auri wani tsoho ne dan kimanin shekara 50, alhali tana da cikin wata 4 da ta boye masa. Shi ne bayan wata biyar a tare da shi ta haife danta namiji a boye, daga bisani ta jefar da shi.
Haka kuma ’yan sandan sun gano cewar wani ne mai suna Umar Lili da ke kauyan Musari ya yi mata cikin, kamar yadda ita Hadiza ta fada masu. Wannan ne ya sanya jami’an tsaron suka kama shi kuma yanzu haka yana hannunsu yana amsa tambayoyi.
Shi kuma mijin matar mai suna Babannan Abdullahi, ya tabbatar da cewar matarsa ta aikata wancan laifi da ake tuhumarta saboda haka da shi da Umar Lili da ita Hadiza suna hannun ’yan sanda suna amsa tanbayoyi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya ce matasa ne da suke wasan kwallo a filin kwallo na Asibitin Guri suka gano gawar jaririn saboda ya fara rubewa, warin gawarsa ya fara addabar matasan, idan iska ta busa. Ya ce gano gawar ke da wuya shi ne matasan suka yi kokarin fadakar da ’yan sanda halin da ake ciki. Ya bayyana cewa da zarar an kammala bincike, za a gurfanar das u gaban kotu.