An kama matar da ta kashe kishiyarta ta kona gawar
Kanwar wadda ake matar ta ce ’yar uwarta ce ta yi amfani da tabarya ta kashe amaryar
An kama matar auren nan da ake zargi da kashe kishirta ta kuma kona gawarta, saboda tsabar kishi.
Kanwarta ta bayyana cewa ’yar uwar tata da ake zargi, ta yi amfani ne da tabarya ta hallaka amarya Fatima, wadda wata biyu ke nan da aka auro ta.
- Masu Keke Napep sun shiga yajin aiki a Maiduguri
- Ta yi wa kishiyarta duka da tabarya, ta cinna mata wuta
- Tafiyar Hawainiya da Buhari ke yi ta yi yawa —Baba-Ahmed
’Yan sanda a Jihar Neja sun cika hannu da matar da ake zargi da danyen aikin ne bayan ta kashe kishiyar tata ta cinna wa gawar wuta ne a ranar Talata.
“Kowacce gidanta daban, amma uwargidar ta je gidan amaryar da ke kusa da nata, ta yi mata duka ta kashe ta, ta kulle gawar a daki, ta cinna mata wuta,” inji wani dan uwan marigayiya Fatima.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Neja, Wasiu Biodun ya ce an tsinci gawar amarya Fatima kwance cikin jini a dakinta an kona wani bangare na jikinta.
“Da muka samu rahoton, nan take muka je wurin, muka kamo kishiyarta mai shekara 24 a gidan, kuma kanwar uwargidar ce ta kashe amaryar ne da tabarya.
“An samu tabaryar a wurin da abin ya faru kuma an fara bincikar wadda ake zargin kafin a gurfanar da ita a gaban kotu,” inji shi.