An kama matar da ta raba wa ’yan biki jarkokin man fetur a Legas
Ana dai tuhumar Mis Ogbulu ne kan tuhume-tuhume har guda hudu.
Jami’an ’yan sanda a Jihar Legas sun kama wata fitacciyar mata mai suna Mis Ogbulu Chidinma Pearl, da ake zargi da raba wa ’yan biki jarkokin man fetur.
An dai gurfanar da ita gaban wata kotun majistire a unguwar Oshodi ta jihar.
- An nada Sanata Ibrahim Ida Wazirin Katsina
- Kayayyaki sun tashi a Najeriya saboda tsadar farashin mai —NBS
Bayanai sun ce ana dai tuhumar Mis Ogbulu ne kan tuhume-tuhume har guda hudu.
Daga cikin tuhume-tuhumen akwai raba wa jama’a man fetur a matsayin tukwicin halartar biki (subiniya) yayin wani biki da ta yi ranar 5 ga watana Maris na wannan shekarar a wani dandalin gudanar da biki mai suna Havillah Event Centre a birnin Legas.
’Yan sanda sun ce laifin yana cin karo sashe na 251(1) da na 168 (1) da kuma na 244 na dokar jihar Legas ta 2015, da kuma sashe na 195 (2)(b) na dokar kulawa da muhalli ta jihar Leagas ta 2017.
Sai dai BBC ya ruwaito cewa an bayar da belin matar kan naira miliyan 2 bayan ta gabatar da wasu mutum biyu da suka tsaya ma ta.
Kotun ta kuma dage zamanta zuwa ranar 24 ga wannan watan na Maris domin ta fara sauraron karar.