An kama matar da ta sayar da kananan yara 42
An cafke wata mata da ta sayar da kananan yara 42 domin aikin bauta a shekaru biyar da suka gabata.
An cafke wata mata da ta sayar da kananan yara 42 domin aikin bauta a shekaru biyar da suka gabata.
Matar mai shekaru 45, wadda ke gudanar da mummunar sana’ar a Jihar Kwara ta sanar da haka ne a caji ofis bayan ’yan sanda sun damke ta a yankin Ijora Badia da ke Jihar Legas.
Ta shaida wa hukuma cewa, “Na sayar da kananan yara sama da 42 ga mutane daban-daban, wadanda yawancinsu a Legas suke.
“Na fi sayar da kananan yara ’yan shekaru 7 zuwa 12 kuma Legas nake kawo su inda suka aikin bauta.”
- Najeriya ta kai Kwata-Fainal bayan ta ba Kamaru taliyar karshe a AFCON
- Isra’ila ta kashe ƙarin mutum 174 a Gaza bayan hukuncin Kotun Duniya
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta ce jami’anta sun kubutar da kananan yara uku, namiji da mata biyu, daga hannun matar.
Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya ce wadda aka kaman ce jagorar wani gungun masu sayar da kananan yara kuma an kama ta ne bayan shafe watanni ana bincike da kuma farautar ta.
Hundeyin ya ce kafin a kama ta, rundunar ’yan sandan jihar Kwara na neman ta ruwa a jallo kan zargin hannunta a bacewar kanana yara.
A cewarsa, an kama ta ne a lokacin da ta kawo wasu kananan yara 52 aikin bauta Legas ba tare da izinin mahaifansu ba.
Jami’in ya ce hukumomin ’yan sandan jihar Kwara sun gano 11 daga cikin yaran da ake nema, a lokacin bincike kuma matar bayyana inda ta kai wasu daga cikinsu, kuma kokarin gano inda ragowar suke.