An kama matasa 19 kan kona gidan Sanata Gaya

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama matasa 19 da ake zargi da hannu a kone gidan Sanatan Kano ta Kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gaya/AjingiGarko Alhaji Abdullahi Mahamud Gaya da gidajen wasu jami’an gwamnati da ke garin Gaya. Kuma ’yan sandan sun ce suna farautar […]

An kama matasa 19 kan kona gidan Sanata Gaya
An kama matasa 19 kan kona gidan Sanata Gaya

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama matasa 19 da ake zargi da hannu a kone gidan Sanatan Kano ta Kudu Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gaya/AjingiGarko Alhaji Abdullahi Mahamud Gaya da gidajen wasu jami’an gwamnati da ke garin Gaya. Kuma ’yan sandan sun ce suna farautar wadansu mutum biyar da ake zargin su ne suka jagoranci kone-konen.
Wakilinmu wanda ya ziyarci garin Gaya, ya ruwaito cewa matasan wadanda suka fito da yawa sun ce Sanata Gaya da Abdullahi Mahmoud sun gaza cika musu alkawuran da suka dauka na yi musu wasu ayyuka a karamar hukumar da suka hada da samar da ruwan sha da hanyoyi da wutar lantarki da kuma samar da aikin yi.
Wani matashi da ya ce bai shiga zanga-zangar ba, mai suna Ahmad Sani Gaya, ya bayyana cewa matakin da matasan suka dauka ya nuna cewa yanzu jama’a na bibiyar yadda wakilansu ke tafiyar da al’amuransu. Ya ce lokaci ya yi da masu rike da madafun iko za su san cewa jama’a na kallonsu kuma suna bibiyar abubuwan da suke yi.
Matasan wadanda suka yi dandazo a kan titin Gaya zuwa Kano dauke da gorori da adduna suna zanga-zangar, sun banka wa wani bene da ake jin na Sanata Kabiru Gaya ne da ke dab da gidan Hakimin Gaya wuta, kuma suka kone masa wani gidan gonarsa da ke kan titin zuwa Kano.
Matasan sun kuma auka wa Sakatariyar karamar Hukumar suna jifa da zage-zage inda ba domin jami’an tsaro ba da sun kone ta.
Masu zanga-zangar sun kuma hana direbobin motar haya da na masu zaman kansu wucewa, inda suka rika kone tayoyin mota a tsakiyar tituna suna cewa “Ba ma yi! Ba ma son Kabiru Gaya! Ba mu da wakilci, gara ya dawo gida!”  Mai magana da yawun matasan, wanda ya kira kansa da Shugaban Matasan, Malam Sagiru danmalam ya ce Sanata Kabiru a tsawon shekarun da ya yi a majalisa bai yi wa jama’ar Gaya komai bai sai dumama kujera.
Ya ce yankin Gaya na fama da karancin wutar lantarki amma babu abin da Sanatan ya yi a kan bukatarsu inda ya ce duk wanda ya kwana ya tashi ya san karamar Hukumar Gaya ta jima a cikin mawuyacin rashin ruwan sha amma Sanatansu da dan majalisarsu sun kasa samar musu da ruwan. Ya soki ’yan majalisar da gaza taimakon jama’ar da suke wakilta sai gasar sayen motoci na kece raini. “Da a ce talakawa ne a gabansu da ba su amince da sayen motocin Naira miliyan 30 ba kamar yadda aka saya musu a kwanan baya ba,” inji shi.
A wata sanarwa da jami’in yada labaran Kabir Gaya, Alhaji Idris Afegbua ya sa wa hannu a Abuja, ta ruwaito cewa, “Sanata Kabiru Ibrahim Gaya yana kasar Amurka lokacin da lamarin ya faru kuma ya danganata lamarin  a matsayin aikin makiyansa a siyasance. Sanata ya gina rijiyoyin burtsatse 12 kuma ya sa Gwamna ya ba da Naira miliya 30 don gyara matsalar rowan yankin.