An kama matasa 2 kan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Ondo

Hukumar za ta gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike.

An kama matasa 2 kan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a Ondo

Jami’an Civil Defence suna atisaye

Jami’an Hukumar Sibil Difens, sun kama wasu matasa biyu, kan zargin su da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a yankin Oke­Igbo a Ƙaramar Hukumar Ile- Oluji a Jihar Ondo.

Wata sanarwa da Kakakin Hukumar a Jihar, Mista Daniel Aidemenbor, ya sanya wa hannu, ta ce an kama matasan biyune bayan samun bayanan sirri.

A wani labarin, Aidemenbor ya ce jami’an hukumar sun kama wani da ake zargin da satar manyan wayoyi na Kamfanin Recline Cable.

Wanda ake zargin mai suna Segun Alao, mai shekara 40 wanda ma’aikacin kamfanin ne, sannan ana zarginsa da satar janareta da silin da da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 3.5

An kama shi ne a titin Araromi da ke garin Akure, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno