An kama matasa 3 kan zargin kashe dilan tabar wiwi a Gombe
Dillalin tabar wiwin ya yi zargin mun kwashe masa kayan sana’arsa bayan ‘yan sanda sun kai samame.
Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta kama wasu matasa 3 a unguwar Gabas da ke garin Deba na Karamar Hukumar Yamaltu bisa zargin kashe wani dilan tabar wiwi saboda sabanin da ya shiga tsakanin su.
Kakakin rundunar a jihar Gombe, ASP Mahid Mu’azu Abubakar ne ya sanar da haka a yayin yi wa manema labarai holen ababen zargin a shelkwatar ’yan sanda a madadin Kwamishinan ’yan sanda Hayatu Usman.
- Kotu ta ba da umarnin sayar da kadarorin surukin Buhari
- Kotu ta aike da Murja gidan gyaran hali kan zargin karuwanci
ASP Mahid ya ce a ranar 12 ga watan Fabarairu 2024 wani mai suna Mustapha Mato ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na garin Deba da cewacfada ya kaure a tsakanin wadannan matasa 3 da wani mai suna Sama’ila Yusuf mai shekara 30 da suka cakawa wuka ya mutu.
A cewar Kakakin ’yan sandan, suna samun wannan rahoto ne jami’ansu suku bazama domin gudanar da bincike, inda suka gano cewa wanda aka kashe din dilan tabar wiwi ne kuma rikici tsakanin sa da kwastomominsa ne ya jawo fada har suka soke shi da wuka ya ce ga garinku nan.
Ya ce ’yan sandan na ci gaba da gudanar da binciken kan wadanda aka kama din kuma da zarar sun kammala za su tura su zuwa kotu.
Aminiya ta zanta da matasan uku wadanda suka labarta mata yadda lamarin ya kasance har ta kai ga mutuwar Sama’ila Yusuf, inda suka ce fada ne ya hada su bayan ’yan sanda sun kai masa samame ya gudu ya bar tabar wiwinsa.
Matasan da ke hannu sun ce bayan faruwar hakan ce washegari Sama’ila ya yi zargin cewa su ne suka kwashe masa tabar wiwinsa da ya tsere ya bari.
Sun ce a dalilin haka ne Sama’ila ya tattaro yara da adduna da wukake inda a garin fada suka soki daya daga cikinsu, sai su ma suka kwace wukar suka caka wa Sama’ila a baya da kuma wuyansa da hakan ya yi sanadiyar mutuwar sa.