An kama matasa da ke shirin auren jinsi
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wadansu da ake zargin ’yan daudu ne su kusan 12 a lokacin da suke tsakiyar gudanar da bikin auren wadasu abokansu guda biyu wadanda suka yi niyyar angwancewa a matsayin miji da mata. Aminiya ta rawaito cewa bikin auren wanda bai samu damar kammaluwa ba sakamkaon samamen da […]

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wadansu da ake zargin ’yan daudu ne su kusan 12 a lokacin da suke tsakiyar gudanar da bikin auren wadasu abokansu guda biyu wadanda suka yi niyyar angwancewa a matsayin miji da mata.
Aminiya ta rawaito cewa bikin auren wanda bai samu damar kammaluwa ba sakamkaon samamen da Hukumar Hisba ta kai wurin da ake gudanar da shi a Dandalin shakatawa na Hills and balley da ke garin Dawakin Kudu cikin Jihar Kano, an shirya gudanar da shi ne tsakanin saurayi Faruk Maiduguri wanda shi ne amarya, da kuma wani saurayin mai suna Abba, wanda ya gudu.
Har ial yau rahotanni sun bayyana cewa ba don jami’an tsaro da suka shiga tsakani ba to da an yi batacciya sakamakon daukar doka a hannu da matasan garin Dawakin Kudun suka yi niyyar yi a kan shiraya bikin a yayin da suka samu labarin abin da ke faruwa a dandalin shakatawa da ke garin.
Mafi yawan mahalarta taron wadanda suka zo daga garuruwa daban-daban na cikin kasar nan sun bayyana cewa sun samu katin gayyatar bikin ne ta hanyar kafar watsa labarai na Whatsapp da kuma BB. Haka kuma sun karyata cewa bikin an shirya gudanar da shi ne da niyyar aure a tsakanin abokan nasu, inda suka ce su sun je wurin taron ne don taya abokinsu Faruk Maiduguri murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Faruk Miaduguri wanda ake zargin shi ne “amarya,” ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin zargin da ake masa na cewar bikin aurensa ake yi, inda ya ce shi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ya shirya gudanarwa. “A wanann shekarar ce na cika shekara 20 da haihuwa, hakan ya sa na shirya gudanar da bikin tare da gayyatar abokai don su taya ni murna. Ban da haka ban san komai a kan zargin da ake mana ba.” Inji shi.
A ganawarsa da ‘yan jarida, Kwamandan Hukumar Hisba Ustaz Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa hukumarsu ta samu labarin bikin auren ne ta hanyar wata kafar watsa labarai da kuma wadansu daga cikin ‘yan uwan Faruk Maiduguri.
Haka kuma Ustaz Daurawa ya bayyana cewa, Hukumarsu ta samu kwafen katin gayyatar bikin auren wanda aka fake da gayyatar bikin ranar haihuwar a cikinsa. “Lokacin da ‘yan uwan Faruk Miaduguri suka sanar da mu halin da ake ciki, ma’ana cewa dan uwansu zai yi auren jinsi, sai muka nemi su ba mu shaida, inda suka kawo mana kwafen katin gayyatar bikin auren wanda aka yi basaja da cewa bikin zagayowar ranar haihuwa ne. Ga abin da aka rubuta a jikin katin,’’ Yau ake Gobe sai labari….’’
Har ila yau, Shuagabn Hisbar ya yi karin haske da cewa akwai kamshin gaskiya a cikin al’amarin na gudanar da auren jinsin, duba da kamannin irin mutanen da suka halarci taron. “ Duk da cewa ba mu kammala bincike a kan lamarin ba, amma akwai kamshin gaskiya a cikin rahoton da muka samu na cewa auren jinsi za a gudanar a tsakanin matasan ba bikin zagayowar ranar haihuwa ba, idan aka yi duba da kamanni da shigar suturar da yananin maganar irin mutanen da suka halarci taron ya yi kama da na ‘yan daudu.” Inji shi.
Ustaz Aminu Daurawa ya kara da bayyana cewa,”Kamar yadda ta saba, Hisba za ta kira iyayen wadannan yara ta zauna da su, domin akwai bukatar gyaran tarbiyyar yaran, wadanda ko da babu zargin aure a kansu to akwai alamun rashin tarbiyya a tare da su.” Inji shi.